AMFANIN GANYEN MAGARYA A JIKIN DAN ADAM

Itaciyar magarya wadda aka fi sani da (Assidir) Da larabci kokuma (Lote) a harshen turance, itaciya ce mai tarihi da albarka tun dadewa Annabi S.A.W ya tabbatar mana da amfaninta.
Magarya na dauke da magunguna masu matukar mahimmanci a jikin dan Adam kuma ta na da karfin kashe kwayoyin cuta cikin dan kankanin lokaci in sha Allah.
Ita Magarya Antibiotic ce mai karfin gaske kuma cikin ikon Allah ba ta da wani illa wato (side effects) na a zo a gani.
Ga wasu daga cikin amfaninta.
1.Ta na magance Ciwon daji (cancer) : Za’a dafa garin magarya a dinga sha da zuma ya na kashe kwayar cutar daji ko da a cikin jini ne.
2.Ta na magance cututtukan fata kamar irinsu tautau, makero,Kazuwa da sauransu.
Za’a dingakwa6awa da zuma ana lsha ana shafawa a Wurin da abin ya shafa.
3.Maganin ulcer idan ana shanta da madara ko zuma.
4.Ta na taimaka wa hanta ya hanata jin ciwo da cututtuka.
5.Ta na tsaida zawo cikin kankanin lokaci idan aka Sha Ganyen da ruwa ko a kunu.
6.Ta na taimaka wa wajen mikar da kasusuwa musamman ga mai karaya.
7.Ta na maganin rashin sha’awa ga mata idan su na tsarki da ita kuma su na sha da madara.
8.Kuma a karshe dai yana warware sihiri a cewar malaman sunna Idan aka jika garin a ruwa tare da karanta wasu ayoyi daga cikin Alqur’ani mai girma.
Abubuwan suna da yawa, idan akwai wasu da kuka sani kuma, ku kara mana.
Yaya Mustyn ku