FASSARAR MAFARKAI GUDA 20 DA MA’ANONINSU

Ma’anoni da sharhi kan mafarkai guda 20 da ake yawan yi, tare da fassarar su a rayuwar yau da kullum.


FASSARAR MAFARKAI GUDA 20 DA MA’ANONINSU

Mafarki wani ɓangare ne na rayuwar dan Adam da ke iya zama alamar alheri ko gargadi. A wannan rubutun, zamu duba fassarar wasu daga cikin mafarkai da ake yawan yi da kuma ma’anoninsu.

1. Mafarkin Kuka da Hawaye

Idan mutum yayi mafarkin yana kuka ko yana hawaye, hakan yana nuna cewa zai samu farin ciki da saukin matsaloli nan gaba.

2. Mafarkin Gawa

Mafarkin ganin gawa yana nufin samun arziki da wadatar dukiya daga wata hanya da ba a zata ba.

3. Mafarkin Fada Cikin Rami

Idan mutum yayi mafarki yana cikin rami ko ya fada cikinsa, yana nuna cewa zai fuskanci wani kunci ko bakin ciki.

4. Mafarkin Tattara Takardu

Idan mutum yayi mafarkin yana tattara takardu, yana nuni da cewa Allah zai buda masa arziki da dukiya mai yawa.

5. Mafarkin Shan Jini

  • Idan mutum yayi mafarkin yana shan jini, yana nuna samun kudi ta hanyar haramun.
  • Idan yana zubawa a wani wuri, yana nuna samun halal da albarka.

6. Mafarkin Kiyashi (Kumburin Jiki)

Wannan mafarki yana nufin sabbin abokai ko sababbin kawaye a rayuwa.

7. Mafarkin Rawa da Nishadi

Idan mutum yayi mafarkin yana rawa da nishadi, yana nuni da cewa zai hadu da bakin ciki nan gaba.

8. Mafarkin Katofawa Wani Yawu

Wannan mafarki yana nuna cewa mutum zai yi nasara akan makiyansa ko abokan gaba.

9. Mafarkin Hadari Yana Hadewa

Idan mutum yayi mafarkin ganin hadari, yana nuna cewa zai samu farin ciki da biyan bukata.

10. Mafarkin Cin Naman Kaza

Wannan mafarki yana nuni da samun babban arziki cikin kankanin lokaci.

11. Mafarkin Shan Zuma

Idan mutum yayi mafarkin yana shan Zuma, yana nuna cewa zai sami rayuwa mai albarka da biyan bukatu.

12. Mafarkin Hakori Ya Fita

Idan mutum yayi mafarki cewa hakorinsa ya fita, yana nuna cewa zai yi rayuwa mai tsawo.

13. Mafarkin Hayaki Yana Fita Daga Wani Gida

Wannan mafarki yana nufin cewa mutum zai samu arziki mai yawa a wannan shekara.

14. Mafarkin Shan Ruwa

  • Idan ruwan yana da sanyi, yana nuni da wadata da arziki.
  • Idan yana dumi, yana nuni da wahala ko kunci.
  • Idan yawan ruwa yana da yawa, yana nuni da tsawon rai.

15. Mafarkin Wanka da Ruwan Marmaro

Wannan mafarki yana nuni da cewa bukatar mutum zata biya cikin kankanin lokaci.

16. Mafarkin Ciwon Hannu

Idan mutum yayi mafarkin yana jin ciwon hannu, yana nuna cewa zai sami kyauta daga sirikinsa ko wata kyauta ta musamman.

17. Mafarkin Guguwa Ta Wuce Ta Gabanka

Yana nuni da cewa wani mutum da ya dade baya gari zai dawo gida.

18. Mafarkin Haihuwar Tagwaye

  • Idan mutum yayi mafarkin cewa matarsa ta haifi tagwaye, yana nuna cewa zai samu bunkasar arziki.
  • Idan mace tayi mafarkin ta haifi tagwaye maza, mijinta zai nuna mata kauna sosai.

19. Mafarkin Babban Gida

Wannan mafarki yana nuna cewa mutum zai sami karuwar arziki ko habakar dukiyarsa.

20. Mafarkin Wasa da Wuka

Idan mutum yayi mafarkin yana wasa da wuka, yana nuna cewa zai samu kudi kuma zai kasance mai yawan kyauta da taimako.