HATIMIN HASBUNALLAHU WANI’IMAL WAKILU – Kariya daga Sihiri da Mummunan Baki

HATIMIN HASBUNALLAHU WANI’IMAL WAKILU – Kariya daga Sihiri da Mummunan Baki

Idan kana son kariya daga sihiri, mugun baki, ko duk wani mummunan abu a jikinka ko gidanka, ga wata ƙaƙƙarfan hanya da za ka bi:

1. Rubuta wannan hatimi:

“Hasbunallahu wa ni’imal wakilu ‘alaihi tawakkaltu wa huwa Rabbul ‘Arshil Azim”

2. Yawan rubutun:

Kafa 41

Hatimin kafa 11

3. Yadda ake amfani da hatimin:

Wanke rubutun da ruwa.

Samu madarar shanu (nono).

Samu hatsin gero, a dakashi sau ɗaya.

Hade ruwan rubutun da gero.

Sha kai da iyalanka.

4. Fa’idar yin wannan:

Kariya daga sihiri na tsawon shekaru uku.

Idan aka maimaita sau 3 ko sau 7, babu wani sihiri, mugun bakin mutum, ko tsafi da zai yi tasiri.

Allah zai kauda duk wani sharri daga gareka da iyalanka.

Wannan sirri ne mai ƙarfi kuma yana aiki da izinin Allah. Idan kana son ƴan uwa su amfana, ka tura zuwa group 5 domin albarka ta yawaita.

Allah Ya kare mu daga sharri. Amin