HATIMIN NEMAN BIYAN BUQTA KOMAI GIRMANSA

HATIMIN NEMAN BIYAN BUQATA – SIRRIN SAMUN NASARA DA SAURI

.

Gabatarwa

Akwai lokutan da muke da buƙatar wani abu cikin gaggawa – ko dai aiki ne, arziki, lafiya, ko wata nasara. Idan kana neman hanya mai sauƙi da yardar Allah domin biyan buƙatarka cikin sauri, wannan Hatimin Neman Buƙata na daya daga cikin manyan sirrika masu ƙarfi.

Duk abin da kake nema na alkhairi – Allah zai baka cikin sauƙi da sauri insha Allah.


Yadda Ake Yin Hatimin Neman Buƙata

1. Rubuta Wannan Hatimi a Allo

  • Samu allo ko farin takarda, ka rubuta wannan hatimi sau uku (3).
  • Bayan ka rubuta, sai ka sha ashafe fuska da shi (wato a shafa fuska da hannun da aka riƙe da hatimin).

2. Karanta Wannan Kalma Sau Dubu (1000)

Bayan ka gama shafa fuska da hatimin, sai ka karanta wannan kalma sau 1000:

وَتَقَدَّلْنَا بِهَا جَمِيعَ الْحَاجَاتِ
WATAQADILANA BIHA JAMI’AL HAJATI

3. Aika Sallar Annabi (SAW) & Neman Buƙata

  • Bayan ka gama wirdin kalmar sau 1000, sai ka tafi wajen buƙatarka cikin yarda da Allah.
  • Ana so ka yawaita salatin Annabi (SAW) kafin da bayan yin wannan aikin.

Fa’idar Wannan Hatimi

Neman aiki – Idan kana son aiki a gwamnati ko ko’ina, yana da amfani.
Samu biyan bukata cikin sauri – Idan kana da wata buƙata mai muhimmanci.
Neman arziki & sauƙin rayuwa – Idan kana fuskantar wahala.
Samun nasara a rayuwa – Idan kana son yin nasara cikin halal.

Idan ka aikata wannan da zuciya daya, Allah zai baka bukatarka cikin sauri!


Kammalawa

Wannan sirri an gwada shi an tabbatar da ingancinsa. Duk wanda ya bi wannan hanya da niyyar neman alkhairi zai ga sakamako mai kyau.

Allah ya biya mana bukatunmu, ya albarkaci rayuwarmu, ya ba mu nasara a duniya da lahira. Amin.


Raba Wannan Albarka

Idan kana son karin albarka da lada, ka raba wannan sirrin zuwa wasu groups biyar (5) domin suma su amfana. Allah ya taimake mu, Amin.