MAGANIN BARAWO WANDA ZAI DAWO DA KAYAN DA YASATA DAKANSA

  • MAGANIN BARAWO DOMIN MAIDO DA ABINDA AKA SATA


    Gabatarwa

    Sata na daga cikin fitintinu da ke addabar mutane, musamman manoma da masu kiwon dabbobi. Idan an sace maka dabbarka, akwai wata hanya ta dabi’a da za a iya amfani da ita domin maido da ita cikin yardar Allah. Wannan hanya tana aiki ne akan dabbobi da ake daurewa da igiya kamar shanu, tumaki, awaki, da makamantansu.

    Muhimmin Bayan: Wannan magani ba ana amfani da shi wajen komai ba. Ba’a amfani da shi wajen dawo da kayayyaki kamar kudi, waya, ko kayan gida.


    Yadda Ake Yin Maganin Maido da Dabba

    1. Rubuta Wannan Ayar a Takarda

    A dauki takarda mai tsafta a rubuta wannan ayar daga Al-Qur’ani:

    (إن لك ألا تجوع فيها ولا تعرى)
    (Innalaka Alla Taju’a Fiha Wala Ta’are)

    Za ka iya rubuta ayar sau daya, sau uku, sau bakwai, ko sau goma sha daya – amma yawan rubutun ya kasance mara (wutiri), wato ba lissafin biyu, hudu, shida ba.

    2. Yin Laya da Saka Ta a Turken Dabba

    • Bayan ka gama rubutawa, ka nade takardar ka sanya ta cikin wata leda mai kyau domin kariya daga ruwa.
    • Ka je wajen turken dabbar da aka daure ta a baya, ka daure layar ajikinsa ko a jikin wata igiyar da ke kusa da wurin.

    3. Yin WIRDIN Ayar

    Bayan ka daure layar a wurin, sai ka fara wirdin ayar ta hanyar karantawa akai-akai yadda kake iyawa.

    Wallahi, idan har ba a yanka dabbar ba, to duk inda aka kaita, zata dawo gidan da aka sace ta!


    Kammalawa

    Wannan hanya an gwada ta an tabbatar da ingancinta. Idan har dabbarka ba a yankata ba, cikin ikon Allah zata dawo gida da kanta.

    Allah ya karemu daga masifa da fitina, ya tsare mu daga barayi, kuma ya kare mana dukiyoyinmu. Amin.


    Raba Wannan Sirrin

    Idan kuna son karin albarka da lada, ku raba wannan sirrin zuwa wasu groups biyar domin suma su amfana. Allah ya taimaka, Amin.