MAGANIN KARATU DA HADDA MAI KARFI MUJARABUN

Maganin Karatu da Hadda Mai Karfi (Mujarabun)

Idan mutum – yaro ko babba – yana karatu amma baya fahimta, yana yawan mantuwa ko kuma baya iya haddace abubuwan da yake koyon su, wannan sirri zai taimaka masa da izinin Allah.

Hanyoyin Yin Wannan Magani:

  1. Rubuta wadannan ayoyi guda bakwai – Ko wacce aya a rubuta ta sau bakwai kamar yadda aka nuna a ƙasa.
  2. Yi amfani da ruwa mai tsarki – Ruwan Zamzam, ruwan sama ko ruwan dutse sufi kyau.
  3. Wanke rubutun da ruwan – Bayan an gama rubuta ayoyin, sai a wanke rubutun da ruwan sannan a sha.
  4. Yi hakan na tsawon kwana bakwai – Idan hakan yayi yawa, za a iya yin sa na kwana uku ajere.
  5. A sha kafin karin kumallo – Ana shan ruwan rubutun kafin karin safe kowacce rana.

Ayoyin da za a rubuta:

  1. بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
    Wa salla Allahu ala Nabiyyil Kareem
  2. وَقُلْ رَبِّ زِدْنِي عِلْمًا (7x)
  3. لَا تُحَرِّكْ بِهِ لِسَانَكَ لِتَعْجَلَ بِهِ (7x)
  4. إِنَّ عَلَيْنَا جَمْعَهُ وَقُرْآنَهُ (7x)
  5. فَإِذَا قَرَأْنَاهُ فَاتَّبِعْ قُرْآنَهُ (7x)
  6. ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا بَيَانَهُ (7x)
  7. سَنُقْرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰ (7x)
  8. إِنَّهُ يَعْلَمُ الْجَهْرَ مِنَ الْقَوْلِ وَيَعْلَمُ مَا تَكْتُمُونَ (7x)

Amfanin Wannan Magani:

Zai hana mantuwa da jahilci
Zai sa mutum ya fahimci karatunsa da sauri
Zai taimaka wajen haddace Al-Qur’ani ko kowanne irin karatu
Zai kawo son karatu da basira

Kammalawa:
Wannan magani ne mai matukar amfani ga duk wanda ke son haddace ilimi cikin sauki. Idan an bi wannan tsari, matsalar haddacewa da mantuwa zata kare da izinin Allah.

Allah Ka cigaba da yi mana jagoranci a cikin dukkanin al’amurranmu. Ameen.