Sassaƙen Itatuwa da Amfaninsu

Sassaƙen Itatuwa da Amfaninsu
Gabatarwa
A cikin hikimar halitta, Allah ya hore mana bishiyoyi masu albarka waɗanda sassaƙensu ke dauke da magunguna na gargajiya. Ana amfani da sassaken bishiyoyi domin warkar da cututtuka daban-daban, tun daga ciwon jiki, basir, tari, zuwa matsalolin ciki da mafarkin yara. A nan za mu kawo wasu daga cikin sassaken bishiyoyi da amfaninsu ga lafiyar dan adam.
1. Sassaƙen Ƙirya
✅ Yadda ake amfani da shi: A jika sassaken ƙirya a cikin ruwa na wani lokaci, sannan a sha.
✅ Fa’ida: Yana maganin ciwon jiki da kuma rage raɗaɗin jiki.
2. Sassaƙen Taura
✅ Yadda ake amfani da shi: A jika sassaken bishiyar taura a cikin ruwa, sannan a sha.
✅ Fa’ida: Yana maganin tamama (jin-kashi) da yara ke fama da shi, yana kuma karfafa kashi.
3. Sassaƙen Marke
✅ Yadda ake amfani da shi:
- A jika sassaken marke a ruwa a ba wa mata masu ciki idan suna fama da ciwo.
- Ana shanya sassaken ya bushe a daka, a hada da irin gero idan za a shuka don kyakkyawan sakamako.
- A hada sassaken marke da jar-kanwa a sha domin maganin tari da kinkiba.
✅ Fa’ida: - Yana taimakawa lafiyar mata masu ciki da jaririn da suke dauke da shi.
- Yana kara ingancin shuka.
- Yana maganin tari da kinkiba.
4. Sassaƙen Shirinya
✅ Yadda ake amfani da shi: A jika sassaken da ruwa a rinka ba wa yara su sha.
✅ Fa’ida: Yana maganin mafarkin yara.
5. Sassaƙen Tumfafiya
✅ Yadda ake amfani da shi: A kankare sassaken tumfafiya a hada da nono a sha.
✅ Fa’ida: Yana maganin shawara.
6. Sassaƙen Bakin Maƙarho
✅ Yadda ake amfani da shi: A jika sassaken bakin maƙarho a cikin ruwa har tsawon kwanaki uku, sannan a sha.
✅ Fa’ida: Yana maganin basir mai tsiro.
7. Sassaƙen Marke (Maganin Tari)
✅ Yadda ake amfani da shi: A sassako bishiyar marke, a dafa shi da ruwa, idan ya huce a hada da lemon tsami sannan a sha.
✅ Fa’ida: Yana maganin tari.
8. Sassaƙen Farar Dorawa da Sassaken Mangwaro
✅ Yadda ake amfani da su: A jika su tare da jar-kanwa sannan a sha.
✅ Fa’ida: Yana maganin basir.
9. Sassaƙen Kwanarya
✅ Yadda ake amfani da shi: A dafa shi da nonon saniya sannan a rika sha. Bayan an sha, ana yin amai.
✅ Fa’ida: Yana maganin shawara.
10. Sassaƙen Gawo
✅ Yadda ake amfani da shi: A jika sassaken gawo da ruwa sannan a sha.
✅ Fa’ida:
- Yana maganin taurin kai, musamman ga matasa masu yawan taurin kai ko ‘yan daba.
- Yana sanya nutsuwa da kwanciyar hankali.
11. Sassaƙen Goba, Mangwaro da Lemon Tsami
✅ Yadda ake amfani da su: A shanya su su bushe, sannan a daka, a rika jikawa da ruwa ana sha.
✅ Fa’ida: Yana maganin ciwon ciki.
12. Sassaƙen Ararraɓi
✅ Yadda ake amfani da shi:
- A jika sassaken Ararraɓi sannan a sha.
- A shanya shi ya bushe, a daka, sannan a rika barbadawa a wurin da cutar tau-tau ta fito.
✅ Fa’ida: - Yana maganin tau-tau.
Kammalawa
Allah ya hore mana bishiyoyi masu albarka waɗanda sassakensu ke dauke da magunguna masu amfani ga jikin ɗan adam. Yana da kyau mu kula da lafiyarmu ta hanyar amfani da waɗannan magungunan gargajiya da kuma kiyaye tsafta.
Idan ka amfana da wannan bayani, kada ka manta ka tura zuwa ga sauran ‘yan uwa domin su ma su amfana!