SIRRIN SALATIN ANNABI (S.A.W)

SIRRIN SALATIN ANNABI (S.A.W)

SIRRIN SALATIN ANNABI (S.A.W)

A daren Mi’iraji, Manzon Allah (S.A.W) ya ga wani mala’ika mai hannaye dubu, kuma a kowane hannu akwai yatsu dubu. Babu wani aiki da yake yi sai ƙirga da ƙididdiga. Sai Manzon Rahama (S.A.W) ya tambayi Jibrilu (A.S):

“Ya Jibrilu, wane mala’ika ne wannan?”

Sai Jibrilu (A.S) ya amsa da cewa:

“Wannan shi ne mala’ikan da ke kula da duk wani digon ruwa da yake sauka a ƙasa, yana ƙirgawa.”

Sai Annabi (S.A.W) ya matsa kusa da shi ya ce:

“Yanzu ka san dukkanin digon ruwan da ya sauka tun daga halittar duniya?”

Sai mala’ikan ya ce:

“Na rantse da wanda ya aiko ka da gaskiya! Na san yawan digon da ya sauka a Sahara. Na san yawan digon da ya sauka a fako. Na san yawan digon da ya sauka a gona, lambu, maqabartu, da wanda ya sauka a ƙasa da filayen duniya gaba ɗaya.”

Sai Manzon Allah (S.A.W) ya yi mamaki ya ce:

“Lallai kana da ƙaifin haddacewa da riƙe lissafi!”

Sai mala’ikan ya ce:

“Ya Rasulallah (S.A.W), amma akwai abu guda ɗaya da na kasa ƙirga shi, duk da iyakar ƙwazon ƙididdigata!”

Sai Manzon Rahama (S.A.W) ya tambaye shi:

“Mene ne wannan abin da ya gagare ka?”

Sai mala’ikan ya amsa:

“Wani abu ne da wasu mutane daga cikin al’ummarka suke yi. Idan suka taru suka ambaci sunanka suna yin salati a gare ka, to ladansu a wajen Allah (S.W.T) ya fi ƙarfina, har yau na kasa ƙididdige shi!”

Ya Allah (S.W.T), ka dawwamar da zuciyoyinmu da yin salati ga Annabi Muhammad (S.A.W).

Ya ku ‘yan uwa, duk wanda ya karanta wannan sako, ya tura wa masoya Annabi Muhammad (S.A.W) domin a ƙarfafa juna wajen yin salati!