TAKAITACCEN BAYANI A KAN ETHICAL HACKING

TAKAITACCEN BAYANI A KAN ETHICAL HACKING
…ko ka san kullum sai an yi kutse an sace miliyoyin daloli a yanar gizo?
Kuma watakila ka yi kuskure fahimtar mene ne “ethical hacking”, har kana jin tsoron furta shi. To a wannan rubutun zan fede biri har wutsiya cikin sauki.
🌍 Misali, a watan January 2025 an yi kutse wa kamfanin Phemex inda aka sace kimanin $69.1 Million
🌍 Sannan kuma a February 2025 an yi wa Bybit kutse an sace $1.5 Billion
🌍 Haka nan dai a April 2025, an yi wa wani kamfanin Australia kutse inda aka sace $500,000
🌍 Har ila yau, a shekarar 2023 kadai, an yi asarar makudan kudade sama da $12 Billion sakamakon cybercrime
🌍 Bugu da kari, a wannan shekarar ta 2025 kadai an sace kudade kimanin $2 Billion.
💠 To, Da Farko Mene ne Ethical Hacking?
Sabanin yadda mutane suke tsorata idan sun ji an ce “ethical hacking”, abun da yake nufi shi ne amfani da ilimin hacking don ba da tsaro ba don cutarwa ba. Ana kiran wadannan mutane da “ethical hackers” ko “white hat hackers.” Suna aiki da izinin system owners don detecting vulnerabilities da gyara su kafin miyagu su shiga su yi barna 🎯
💠 Ire-iren Hackers
1 — White Hat Hackers: Wadannan su ne ethical hackers. Suna amfani da iliminsu don taimakawa wajen inganta tsaro. Misali, white hat hacker zai iya kokarin hacking wani banki, idan ya samu vulnerability sai ya yi reporting don a gyara saboda kar miyagu su samu kofar yin barna. Ana iya kiransu testers ko bug hunters ko ethical hackers. Misali: su ne jami’an tsaro masu gaskiya.
2 — Black Hat Hackers: Wadannan kuma su ne hackers din da ke yin kutse don mugunta, watakila don su yi sata, ko destroying information, ko haifar da wata matsala, ko leken asiri da sauran miyagun ayyuka na barna. Misali: su ne ‘yan ta’adda ko ‘yan fashi.
3 — Gray Hat Hackers: Su kuma wadannan suna tsakanin white hat da black hat. Suna iya yin kutse ba tare da izini ba, amma ba koyaushe suke da manufar cutarwa ba. Sometimes ya kan iya acting kamar mai gaskiya, idan ta juye kuma sai ya canja taku. Misali: da farko jami’in tsaro ne, idan ya bi son zuciya kuma sai ya yi corruption.
Ethical hacking yana da muhimmanci saboda yana taimaka wa wajen inganta tsaro, saboda kullum a duniya sai an kai hare-hare an sace makudan kudade da sauran miyagun ayyuka. Don haka kowanne kamfani yana matukar bukatar ethical hacker a kusa da shi 📌
💠 Yaya Ake Zama Ethical Hacker?
—Da farko idan kana son zama ethical hacker kana bukatar computer. Kar ka ce waya ce da kai, ko iPhone/Google Pixel/Samsung ba za su yi ba!
—Na biyu, ka fara karantar ilimin Cybersecurity, musamman na flowdiary.com.ng. An koyar da shi daidai misali ga beginners, wato beginner-friendly ne course ne.
—Na uku, ka shiga course din Professional Bug Hunting, shi ma akwai a Flowdiary din. Kwararren masanin tsaro Engr. Ibrahim Auwal ne ya koyar da su duka. A wannan course din aka hade ethical hacking da bug hunting.
Hakika Cybersecurity, Ethical Hacking, da Bug Hunting suna daga cikin manyan skills wadanda duniya take matukar bukatarsu, kamar dai yadda ka ji na ce kowanne kamfani yana bukatarsu. Misali ka dauki Bug Hunting ma wanda ba ya bukatar sai wani kamfani ya ba ka aiki 🏅
Kana da wata tambaya?
Yi sharing ga wasu ↗️
Muhammad Auwal Ahmad
Cofounder & CEO: Flowdiary
10th April 2025